Jinkirta sallah

Egypt's Dar Al-Ifta

Jinkirta sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin jinkirta sallah daga farkon lokacinta a cikin mutane?

Amsa

Jiran mutane ko sauraron  halartansu domin yin sallah yafi dacewa da a ce mutum ya yi sallah a farkon lokaci shi kadai, hakika Bukhari da Muslim sun ruwaito a littafansu daga Muhammad bin Amru bin Alhasan bin Ali bin Abi Dalib Allah ya yarda da su ya ce: “Mun tambayi Jabeer bin Abdallah Allah ya kara musu yarda akan sallar Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam, sai ya ce: ya kasance yana sallatar azahar da tsakar rana, ita kuma sallar la’asar yana sallatanta ne a lokacin rana tana tsaye, magariba kuma idan rana ta fadi, ita kuma sallar Issha’i idan mutane suka yawaita sai ya gaggauta yinta, idan kuma sukayi karanci sai ya jinkirta, ita kuma sallar asuba yana sallatanta ne da jijjifi”.

Alhafeez Al’kasdalani ya ce a cikin littafin “Irshad As-sari” (1/502): {a cikin wannan akwai nuni zuwa ga bayyana jinkirta yin sallah domin halartan jama’a, hakan yafi dacewa da gaggauta yinta a hali na kadaici, ai wannan shi ne ma mafi cancanta, wato shi ne jinkiri domin yawaitar, mutane yafi dacewa}.

Amma duk da hakan: Ya wajaba dukkan mutane su lizimci yin sallah a masallaci a inda aka kebance domin yin sallar a tsakanin kiran sallah da kuma tayar da ikama, sannan da bin hanyoyin da suka dace wurin gudanar da Ibadan, domin kiyaye hurumin bauta da kuma nesanta rarrabuwan kai da sabani.

Share this:

Related Fatwas