Faduwar fidiya ga mai azumi.
Tambaya
A wani yanayi ne fidiyar azumi ta ke fadi akan mare lafiya?
Amsa
Idan mutum Musulmi ya manyanta ta yanda ba zai iya yin azumi ba, ko kuma ya na shan wahala idan ya yi, ko wata cuta za ta iya kamashi sakamakon yin azumin, sannan likita ya shawarceshi da kar ya yi azumin saboda ciwon da yake fama da shi, sannan kuma mutumin bai da wadatar kudin da zai bayar da fidiyar azumin da ba zai iya ba, ko kuma nauyin da yake kansa zai karu sakamakon ware kudin fidiyan, sannan wadanda yake daukan nauyinsu ba za su iya hakuri da rashi ba, to anan fidiya ta fadi akansa, babu bukatar sai ya bayar, saboda ita fidiyar ta na wajaba ne ga mai ikon bayarwa kuma mai hali, ba wanda bai da shi ba.