Nasiha akan kiyaye kyakkyawan zaman...

Egypt's Dar Al-Ifta

Nasiha akan kiyaye kyakkyawan zamantakewa a tsakanin ma’aurata.

Tambaya

Ta yaya zamu iya kiyaye kyakkyawan zamantakewar aure a tsakanin ma’aurata?

Amsa

Rayuwar aure yana ginuwa ne akan natsuwa da rahama da kauna tare da kiyaye  yanayin da kowani sashe yake fiye da ginuwa akan neman hakkoki, ilimin sanin yanayin rayuwa da kyakkyawan dabi’a wanda Shugabanmu Annabi Muhammadu SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya wajabtawa matar aure shi ne da taji tsoron Allah akan mijinta, sannan ta san cewa kyakkyawan zamantakewa da mijinta da hakurinta akan halayyansa akan rayuwar zamantakewa kofa ce daga cikin kofofin shiganta aljanna, haka nan shima mijin wajibi ne ya kiyaye kokarinta, tare da abin da take aikatawa  na hidimar gida da yawa a kullum, ya kasance mai tausayawa gareta, kuma kar ya dora mata abin da ba zata iya ba, to da wannan yanayin da kowani daga cikinsu yake ji na gaskiya to ma’aurata sa zu iya zama cikin yanayi na daidaito tare da aiwatar da abin da Allah ya bukacesu da shi, tare da nesantar duk abin da zai iya kaiwa ga zama agaban alkali, Allah Ta’ala ya ce: (Allah ya na bayar da hikimarsa ne ga wanda ya so duk wanda aka bai wa hikima to hakika an ba shi alheri mai tarin yawa). {Albakarah:269}

Su hukunce-hukunce na shari’a na shari’a da suke rataye da rayuwar ma’aurata ba ta ginuwa akan tsarin da kowani sashe ya rinka neman hakkinsa da shari’a ta bashi akan dan’uwan zamansa, na hakkoki da wajibai, ta yanda shi kadai ne zai kasance akan gaskiya shi kuma dayan koda yaushe yana kan bata, wanda hakan zai sa a dauki hukunce-hukuncen shari’a kamar wata hanya ce da yi wa juna matsin lamba tare da sanyashi mai tankwaruwa akan bukatunsa ba tare da shi dayan yana son sauke nashi wajibin ba.

Share this:

Related Fatwas