Yi wa mamaci addu’a
Tambaya
Shin yi wa mamaci addu’a a bayyanae ake yi ko a sirrance?
Amsa
Ita addu’a kofarta mai yalwa ne, tana iya kasancewa a bayyane ko a boye, kuma ta kowace irin siga Allah yakan budewa mai rokon kofar amsa addu’arsa, kuntata abin da Allah da Manzonsa suka yalwata, to abin zargi ne, yin jayayya akan haka kuma lamari ne da Allah da Manzonsa SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ba sa so, hakika Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya hana yin ja’inja, inda ya bayyana cewa shi Allah idan ya yi shiru akan abu to yana nuna yalwatawa ne akan abun, kuma ramahama ne ga al’umma, Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ce: (Lallai Allah Azza wa Jallah ya farlanta farillai to kada ku tozartasu, sannan ya haramta haramtattun abubuwa to kada ku kekketasu, sannan ya iyakance iyakoki, to kada ku ketaresu, sannan ya yi shiru akan wadansu abubuwa ba don ya manta dasu ba, to kada kuyi bincike akansu). Addaru Kudni.
Don haka ita addu’a da zikiri a hade yafi kusanto da jin cewa ana amsa, tare da motsa zuciyar mai yinsu, kuma yafi haduwa akan abin da ake yi da yake kaiwa ga nuna tsoron Allah da nuna kaskanci a gaban Allah Ta’ala, musamman idan akwai wa’azi, hakika Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ce: (Rahamar Allah tana tare da jama’a) Tirmizi ne ya ruwaito daga Abdullahi dan Abbas.