Yiwa kai addu’ar alkaba’i ko akan yaro ko dukiya
Tambaya
Mene ne hukuncin mutum ya yiwa kansa addu’ar alkaba’i ko yaronsa ko dukiyarsa?
Amsa
Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wa sallam ya hana mutum ya yiwa kansa addu’ar alkaba’i ko dansa ko dukiyarsa ko masu yi masa hidima, an karbo daga Jabeer bin Abdallah, Allah ya kara masa yarda shi da mahaifinsa, yace: Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi wa sallam ycae: (Kar ku yi wa kawukanku mummunar addu’a, hakanan kar ku yi wa ‘ya’yanku mummunar addu’a, hakanan kar ku yi wa masu yi muku hidima mummunar addu’a, kuma kar ku yi wa dukiyarku mummunar addu’a, don ka da ku zo ya yin addu’ar taku a samu dacewa wurin Allah Ta’ala na amsawa) Muslim.