Hukuncin amfani da kayan gyaran jiki.
Tambaya
Mene ne hukuncin amfani da kayan gyaran jiki?
Amsa
Asalin hukuncin abubuwa dai shine halasci, sai dai fa idan wani haramci yazo ya yi musu tabaibayi daga Littafin Allah Ta’ala, ko wata Sunnah ta Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi sallam, idan adon mace ya kasance daga cikin abubuwan da suka halasta ne, da Allah Ta’ala ya halasta, kuma wannan adon ya kasance akwai bukatar yin mafani da wasu kayayyaki na kawa a wasu lokutan wadanda kamfanonin kayan ado suke kerawa to babu haramci a ciki.
Mu a mahanga ta shari’a ba ma ganin laifi akan hakan, wanda za a ce akwai wani abu da zai haramta amfani da irin wadannan abubuwan da wasu kamfanoni suke samarwa, halascin irin wadannan abubuwa yana tabbata ne matukar babu wani abu tare da su da yake cutarwa ga lafiyar mutum.