Hukuncin shari’a wajen amsar makwaf...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin shari’a wajen amsar makwafi

Tambaya

Idan Musulmi ya batar da wani abu da ba nasa ba, shin dole ne ya biya makwafin abin da aka ba shi, mene ne hukunci amsar wannan makwafin?

Amsa

Karban makwafin abin da aka batar ko aka lalata shi ne “al- Iwad”, idan sashen da abin ya shafa suka yanke hukunci akan haka, kaman sashen shari’a, ko masu shiga tsakani domin warware rikici, to ya halatta a yi amfani da wannan abin da aka bayar a matsayin makwafi, ba haramci a ciki, kuma a wurin lamuntar abu babu maganar kuskure ko ganganci, ko kasancewar mutum yaro ne, ko mahaukaci, ko mai barci, ko rashin sani, duka wadannan abubuwa ba su da tasiri a lamuni; inda daukacin malaman fikihu suka hadu akan cewa lamuni abu ne da shari’a ta tabbatar da shi saboda kiyaye hakkoki, da rashin shiga cikin dukiyoyin mutane ba tare da hakki ba, ganin cewa dukiya ginshiki ne na rayuwa. Haka ma sun hadu akan cewa batarwa, ko lalatawa dalilai ne na tabbatar da lamuni; idan wani mutum ya lalata ko ya batar da dukiyar wani da gangan ko da kuskure, lamuni ya hau kansa, shi kuma lamuni a cikin dukiya yana kasancewa ne da kwatankwaci ko makwafi, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Idan za ku rama, to ku rama da kwatankwacin abin da aka yi maku) [an- Nahli: 126], idan kuma abin ba shi da kwatankwaci sai a biya da kimarsa, ana kuma kaddara kima ne a ranar da aka bata ko aka lalata, al’amarin dai yana komawa ne zuwa ga irin yanda alkali ya kaddara, ko wanda zai kwafe makwafinsa.

Share this:

Related Fatwas