Yada bayanan mutane a kafofin sadar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yada bayanan mutane a kafofin sadarwa na zamani.

Tambaya

Mene ne hukuncin mutanen da suke yada bayanan rayuwarsu a kafofin sadarwa na zamani?

Amsa

Yanda masu yada hutuna da bidiyo suke yi a kafafen sadarwa na zamani, wanda ya kunshi tsarin rayuwarsu na kashin kansu da na iyalansu domin samun masu bin shafinsu: idan har abinda suke yadawa ya shafi abinda ake aibata yadawa ne wanda ba a son a sani a tsarin zamantakewa, ko kuma ba a son gani, kamar al’aura da makamancin haka, to yada irin wannan haramun ne a shari’ance, kuma yin haka laifi ne a dokance, saboda a cikin hakan akwai yada alfasha a cikin al’umma ko yiwa al’umma ta’addanci a cikin tsarinsu na zamantakewa.

Amma idan har abinda suke yadawa ya halasta a gani, kuma yada shi zai amfanar da mutane, - kamar dai gabatar da wani kwarewa domin koyo, ko fadakarwa zuwa ga wani kofa daga cikin kofofin alheri- to a irin wannan yadawar babu laifi a cikinsa a shari’ance, tare da kulawa da yanayin al’ada na rayuwar mutanen wurin da akeson yadawa, sannan shi mai yada bidiyon ya kasance kwararre ne akan abinda yake magana akai ko kuma yake yadawa a cikin al’umma.

Share this:

Related Fatwas