Haduwar jama’a lokacin sallar janaza
Tambaya
Shin haduwar jama’a sharadi ne na ingancin sallar janaza?
Amsa
Mutane uku su yi wa gawa sallah ko fiye da ukun ko kasa da ukun ya inganta a shari’ance, saboda yawan jama’a ba sharadi bane daga cikin ingancin sallar janaza, ai sallar ma tana inganta da mutum daya, amma taruwar jama’a abu ne da akeso ko aka sunnanta, akan wannan fatawar ne jumhorin malaman fikihu su ka tsaya akai tare da mazhabobinsu.