Sharudan ingancin sallar janaza.
Tambaya
Mene ne sharudan ingancin sallar janaza?
Amsa
Ita yin sallah ga jana’iza tana daga cikin fardu kifaya a wurin jumhor din malaman fikihu, hakika shari’a mai girma ta kwadaitar da yin sallar jana’iza, haka nan an kwadaitar da raka gawa har zuwa makabarta, an karbo daga Abu Huraira Allah ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya ce: (Duk wanda ya halarci sallar jana’iza yana da lada daya, haka nan duk wanda ya halarci sallar har ya raka gawar zuwa makwancinta to yana da lada biyu), sai aka tambaya: mene ne girman ladan? Sai Manzon Allah ya ce: (kwatankwacin girman manyan duwatsu biyu). An yi ittifaki akan wannan Hadisin.
An shardanta ingancin sallar janaza kamar yanda aka shardantawa sallolin farilla, kamar dai: tsarki daga karamin hadasi da babba, da kuma tsarkin jiki da tufa da wuri daga najasa, tare da suturta al’aura, tare da fuskantar alkibla, da kuma yin niyya.