Zakkah akan kudin da suke rataye da inshora.
Tambaya
Ta yaya ake fitar da zakkar kudin da suke cikin daftarin inshora?
Amsa
Zakkah ba ta wajaba akan kudaden da aka sanya su a daftarin inshora, sai bayan an karba sun zo hannu, zakkah ba ta wajaba ga Musulmi akan abinda bai gama mallakansa gaba daya ba, amma bayan ya amshi dukiyar ta zo hannunsa, sai shekara ta kewawo dukiyar tana hannunsa to zai fitar mata da zakkah idan ta kai nisabi, sannan kuma ya zama sharudan zakkah sun cika ga dukiyar.