Tsawwalawa kan kudin sadaki da tasirin hakan
Tambaya
Mene ne hukuncin shari’a kan tsawwala kudin sadaki da tasirin hakan?
Amsa
Tsananta kudin sadaki ba shi daga cikin sunnar musulunci, saboda asalin manufar yin aure shi ne kamewar saurayi da budurwa daga fadawa mummunar hanya, Annabi Alaihis-salam yana cewa : (Mafi girman mata wurin daraja sune mafi saukin sadaki) {Al’hakeem ne ya ruwaito daga mustadrak}
Abin da ke zama lazimi anan shi ne rashin tsawwala sadakin mace, sai uba ya saukaka sadakin ‘ya’yansa idan suka samu mazaje nagari, wanda hakan shi ne zai kare yaranmu samari da ‘yan mata daga kauce hanya. Hakika Manzon Allah S.A.W. ya gabatar mana da nasiha mai girma a cikin fadinsa : (Idan wanda kuka aminta da addininsa da dabi’arsa yazo neman yarku to ku aurar masa, idan ba haka ba to zai zama fitina da barna a bayan kasa) {Tirmizi ne ya ruwaito}.