Ragon suna ga namiji da mace
Tambaya
Mene ne hukuncin yanka ragon suna ga namiji da mace?
Amsa
Yanka ragon suna sunna ce mai karfi daga shugabanmu Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), lallai ya kwadaitar da mu akan haka, a asalin yanda abin yake shi ne a yanka tunkiya guda daya ga duk wanda aka Haifa namiji ko mace ba tare da bambanci ba, haka Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi wa dansa Ibrahim, da ma jikokinsa guda biyu masu tsarki Alhassan da Husaini (Allah ya kara masu aminci); an ruwaito Hadisi daga Ibn Abbas (Allah ya kara yarda da su) cewa: Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yanka wa Alhassan da Husaini kowannensu rago guda daya) [Abu Dawud].
Cikan al’amarin kuma shi ne namiji a yanka masa raguna guda biyu, mace rago guda daya, wannan kuma shi aka ruwaito daga jamhur din sahabbai (Allah ya kara yarda da su), haka kuma akwai wasu daga cikin ruwayoyi daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) wadanda suka kwadaitar akansa, amma idan an yanka wa kowanne rago daya ma ya isa, ya kuma dace da sunna; saboda Hadisin Ummu Kurzin (Allah ya kara yarda da ita) ta ce: Na ji Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Yaro namiji raguna guda biyu masu daidai da juna, ‘ya mace kuma rago daya) [Maruwaita Sunan] da kuma wannan ne muke bayar da fatawa.