Ramukon sallah a lokacin da ya wuce.
Tambaya
Shin ya halasta musulmi ya rama abin da ke gareshi na sallolin da suka wuce a lokutan da shari’a ta hana yin sallah a cikinsu?
Amsa
Rama salloli da suka wuce a lokacin da aka karhanta ba ya zama abin hani a shari’ance, kuma ba abun ki ba ne saboda hadisin Anas bin Malik (Allah ya kara masa yarda) in da ya ce: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan dayanku ya yi barci akwai sallah a kansa ko kuma ya rafkana akan gabatar da ita to ya sallaceta a duk lokacin da ya tuna, saboda Allah yana cewa: “ka tsayar da sallah a duk lokacin da ka tuna Allah”) Muslim.
Umurnin da ya zo akan haka na bai daya wurin rama salloli da suka wuce ya amfanar da halascin rama sallah a kowani lokaci koda kuwa a lokacin da aka haramta yin sallah a cikinsa ne, akan wannan jumhorin malaman fikihu suka tsaya.