Mayar da kayan bashi idan ya kasance zinare ne.
Tambaya
na karbi wasu kayayyakin zinare daga wurin abokina a matsayin bashi tun tsawon lokaci, to ya ya zan mayar masa da hakkinsa yanzu?
Amsa
Ya wajaba ga wanda ya ci bashi ya mayar wa da wanda ya amshi kayan zinaren wurinsa da kwantankwacin zinaren da ya amsa tare da kimanta nauyinsa ko kuma abin da ya yi daidai da kimarsa a lokacin mayarwar idan har aka samu fahimtar juna tsakanin mai bashin da wanda ake bi bashin.