Karatun mace mai jinin istihada ga Alkur’ani Mai girma.
Tambaya
Mene ne hukuncin karanta Alkur’ani Mai girma ga macen da ta ke jinin istihadah?
Amsa
Shi dai istihada wani yanayi da jini kan zubowa mace ba a lokacin al’adanta ba, kuma ba a lokacin biki ba, wato haihuwa, to babu wani hukunci irin na haila da aka sanyawa mai jinin istihada, saboda shi wani yanayi ne dan karami, don haka ya halasta ga mace ta karanta Alkur’ani Maigirma, idan kuwa tayi alwala to ya halasta ta taba mushafi na Alkur’ani rubutacce da hannunta.