Tsarin iyali

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsarin iyali

Tambaya

Mene ne hukuncin tsarin iyali?

Amsa

Tsarin iyali da nufin nesanta tsakanin lokutan daukar ciki domin kulawa da lafiyar uwa da kiyayeta daga cutar da yawan daukar ciki a jere yake haifarwa, ko kuma ayi tazara domin uwa ta samu daman kulawa da yaran da ta haifa a farko, to wannan halas ne, kuma ana bukatar irin haka a shari’ance, domin nassosin sunnah masu girma sun bukaci da ayi hakan, domin hakan kiyasi ne akan yin azalo, wanda haka yake nufin wani abu da ma’aurata suke aikatawa a tsakaninsu bisa amincewarsu domin hana daukar ciki da kuma tsarin iyali, kamar dai yanda yazo a ruwayar Imam Muslim a ‘Sahihinsa’ daga Jabir Allah ya kara masa yarda, cewa sahabbai – Allah ya kara musu yarda- sun kasance suna yi wa matayensu azalo da kuyangunsu a lokacin Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam, da labarin haka yaje gareshi bai hanasu ba.

Share this:

Related Fatwas