Tufafin shari’a
Tambaya
Mene ne sifar tufafin da shari’a ta amince wa mace Musulma?
Amsa
Abin da kowa ya sani ne cewa hijabi wajibi ne a shari’ar Musulunci, Allah a cikin Alkur’ani mai girma ne ya bayar da umurnin yinsa, a inda Madaukakin sarki ya ce: (Ka kuma cewa Muminai mata su rufe idanuwansu, su kuma kiyaye al’aurarsu, kada kuma su bayyana adonsu, sai dai wanda ya saba bayyana a al’ada, su rufe kawuwansu zuwa jikkunanku..) [an- Nur: 31], tufafin Musulunci da aka bukaci mace Musulma ta sanya shi ne duk wani tufafi da ba ya bayyana wuraren fitina a jiki, ba kuma sharara da ake iya ganin abin da yake ciki ba, ya zama ya rufe dukan jiki, banda fuska da tafukan hannu, haka ma kafafuwa guda biyu a wajen wasu malaman fikihu, babu laifi idan mace ta sanya tufafi masu launi iri- iri da sharadin kada su zama masu jan hankali, ko masu tayar da fitina, idan wadannan sharuddan suka samu a tare da kowane irin tufafi, to ya halatta mace ta sanya ta fita da shi.