Tambaya
Mene ne hukuncin mata su rufe mace ‘yar’uwarsu bayan ta rasu a makwancinta?
Amsa
Ba laifi bane a shari’ance mata suyi wa mace musulma ‘yar’uwarsu sutura su birneta a kabari, hakan yana tabbata ne a lokacin da babu mazan da za su yi wannan aikin.