Tsattsauran ra’ayi da ta’addanci

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsattsauran ra’ayi da ta’addanci

Tambaya

Mene ne tsattsauran ra’ayi, kuma mene ne ta’addanci?

Amsa

Kalmar “al- Taɗarruf” a harshen Larabci ta samo asali ne daga kalmar “al- Taɗarraf”, kuma suna ne da ake faɗa wa duk abin da ya rangwafa ya koma gefe, ko ya wuce iyaka, bai daidaita ya zama a tsakiya ba, ta haka ne kuma aka kira ƙungiyoyin da suke da tsanani da sunan “al- mutaɗarrifa” ma’ana masu tsattsauran ra’ayi, saboda ba su zama a tsakiya ba, sun ma wuce iyaka ne, lallai Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Kaman haka ne muka sanya kuka zama al’umma matsakaiciya..) [al- Baƙra: 143]. Ita kuwa kalmar “al- Irhab” a harshen Larabci tana nufin tsoratarwa, tana kuma da fuskoki biyu idan mun yi la’akari da hanyoyin da ake amfani da ita.

Fuska mai kyau: Kaman inda Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Ni kawai ya kamata ku ji tsoro) [al- Baƙra: 40], inda a nan Allah yana tsoratar da bayinsa ne akan kada su saɓa alƙawarin da suka ɗauka masa, haka ya zo a cikin addu’ar da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake yi, cewa: (Na kuma jingina bayata zuwa gareka, saboda kwaɗayi da kuma tsoron da nake yi maka..). Fuska mara kyau: Kaman inda Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: (Sai ya ce: ku jefa, lokacin da suka jefa sai suka yi wa idanuwan mutane suddabaru, suna tsorata su, suka zo da babban tsafi) [al- A’araf: 116], ta nan ne ake kiran ƙungiyoyin da suke aikata laifuffuka, suke bin hanyoyin tashin hankali da kisa da lalata kayayyakin al’umma, suke kuma yaƙar gwamnatoci da al’umma saboda biyan buƙatansu na siyasa da sunan ‘yan ta’adda.

Share this:

Related Fatwas