Dakushe hatsarin ayyukan ta’addanci.
Tambaya
Wasu hanyoyi ne kwararru suke ganin za su taimaka wurin dakushe hatsarin tsattsauran ra’ayi tare da kiyaye al’umma daga sharrin haka?
Amsa
Lallai hanyar kalubalantar ayyukan da suke ruguza zaman lafiyar dan Adam tare da mayar da shi koma baya to shi ne a samu taimakekeniya da agazawa juna tsakanin kasashen duniya, sannan kuma dukkan kasashe da suka waye su mike tsaye ta hanyar cibiyoyi na kasa da kasa da kuma na hukumomi na addini domin kalubalantar duk wani salo na tsattsauran ra’ayi da ta’addanci tare da gina wani tsari domin samun kariya daga hakan, tare da sanya wasu hanyoyi da suka dace domin kalubalantar kasashen da suke goyawa ta’addanci baya ko kuma suke tura musu da kudade tare da ba su kariya ta hanyoyin da suka dace, musamman bayan tantance ayyukan tsaurin ra’ayi da ta’addanci na tashinsu daga halin daidaikun mutane wadanda ba a sansu ba zuwa gungun mutane da suke da tsari har suke da kawance da wasu kungiyoyi na duniya wadanda ba ruwansu da muhimmancin al’adu da jin kai ko kuma lamuran addini, babu shakka wannan lamarin ya samar da rashin zaman lafiya a kasahen wannan yanki da na Larabawa da yawa.
Wata kila daga cikin muhimman hanyoyin kalubalantar yanayin tsattsauran ra’ayi da ta’addanci shi ne fuskantar tunanin da yake kaiwa ga shiga ayyukan, ya kamata ga hukumomin da alhakin yaki da su ya rataya a wuyansu da su matsa sosai wurin fafatawa da ‘yan ta’adda bisa tsari da nazartan hanyoyi na zamani da suka dace wadanda suka ketare matakin mayar da martani da zance zuwa matakin warware zantuttukansu da kuma bibiyan wadannan ra’ayuyyuka tsaurara ta mabubbugansu domin
Sanin wasu saddabarunsu a tarihance da zamantakewarsu don kakkabe su daga cikin al’umma, wanda gane hakan shi zai magance yawan hatsarin dake tattare da su mai muni, wata kila cibiyoyi na addini na daga cikin sahun farko da ya kamata a sanya a gaba domin kalubalantar masu irin wanann ra’ayi na ta’addanci.