tsattsauran ra’ayi na tunani
Tambaya
Mene ne tsattsauran ra’ayi na tunani, kuma menene alamomin hakan?
Amsa
Shi tsattsauran ra’ayi na tunani yana nufin mataki ne na farko a matakai na tsaurin ra’ayi, a wancan matakin mai tsattsauran ra’ayi ya kan dauki wata hanya ta sabuwar tunani na wasu halayya wanda ya saba da fahimtar kowa a cikin al’umma, kai harma da babbar kungiyar da yake yiwa biyayya.
Shi mai tsattsauran ra’ayi a wurin tunani gamsuwarsa takan fara ne da nesantar iyakoki da daidaito a hankali, sai fara kusantar wuce iyaka da rungumar hukunce hukunce masu cin karo da gaskiya, misali wanda ke nuna tsananin nuna kiyayya ga mutane bakar fata yakan fara nuna haka ne ta hanyar daukan ra’ayin tunanin da kuma halayyar hakan tun farko wanda yakan zarce yanayin tsarin zamantakewa na bai daya, wanda yake yakar nuna irin wannan halin, hakanan lamarin yake ga mai tsattsauran ra’ayi na addini da waninsa.
Shi tsattsauran ra’ayi na tunani wani ta’addanci ne mai alamar jiji da kai ga mutum daya, inda ya kan ji hakan aransa, ko kuma mutane da yawa su kan ji irin haka ga wani mutum daban, shi wannan mutumin na daban din shin ya kasance mutum daya ne ko mutane da yawa ko shugabanci ne ko kuma wata al’umma ce ko wata kasa ko wasu tarin kasashe daban.
Tsattsauran ra’ayi na tunani yana bin hanyar yada ra’ayuyyuka ne marasa makama a sharia ko doka na cikin kasashe ko na waje, manufar hakan dai shi ne sanya kokwanto a kan manufofi da abubuwan alfanun jama’a da tsare tsare da akidu domin samun alfanu kididdigaggu ko masu yalwa ta hanyoyin da ba su kamata ba.
Hakanan tsattsauran ra’ayi na tunani ya kan yi tasiri a tsaron mutum daya da mutane da kasa da kuma al’ummu na duniya ta mummunar hanya, kamar yanda hakan ke kaiwa zuwa ga girgiza harkar tsaro a sashen tunani da wayewa, da kuma tayar da zaune tsaye da tsattsauran ra’ayi da ta’addanci ta wani sashe na hakan.