Raka jana’iza
Tambaya
Mene ne hukuncin raka jana’iza, wasu abubuwa ne ake so a yi, mene ne ladubban da suka jibinci haka?
Amsa
Shari’ar Musulunci ta kwadaitar akan raka jana’iza, hakan yana cikin sunnoni mustahabbai a wurin jamhur din masana Fiqihu, raka jana’iza yana cikin hakkokin Musulmi akan dan uwansa, ana kuma neman abubuwa da dama da suka hada da:
Yi wa mamaci sallah, da daukan gawarsa, da raka ta har zuwa inda za a rufe ta.
Gaggarwa da rige- rigen daukanta zuwa kabari.
Lizimtar tsoron Allah.
Kada a hada da koke- koke ko kururuwa.
Kada a shagala da maganganun duniya a lokacin raka ta.
An so a tsaya a kabarin mamaci a nema masa gafara a yi masa addu’ar samun rahama da tattaba wajen bayar da amsa.
Duk wanda ya cika wadannan sharudda duka zai sami lada mai yawa da girma.