Bayani akan Asha’ira
Tambaya
Su wane ne Asha’ira, kuma mene ne hukuncin wanda yake sifanata su da kalaman batanci?
Amsa
A farko dai, su shugabanni na Asha’ira su ne wadanda suke bayyana akidar magabata kamar dai yanda take, sannan suka kafa hujjoji da dalilai domin karfafa wancan akidar ta magabata inda suka daga tutarta a gaban masu son zuciya da kungiyoyin bata wadanda suke danganta kansu ga Musulunci, ko kuma agaban wadanda ba Musulmai ba malahida wadanda suke nuna kiyayya ga Musulmai a cikin akidunsu, hakika Asha’ira sun dauki tafarkin kafa hujja da ya hada dalilai na nakali da hankali wanda yake mayar da abu na zato (zanni) zuwa ga na yankan shakku (kada’i) amma ba sa amsa ko amfani da wani dalili na zanni domin tabbatar da wani lamari na tushen akidu, hakika jumhorin shugabanni na Musulmai sun tafi akan wannan mazahaba ta su a tsawon karnoni, kuma su ne mafi yawan al’umma kuma rukuni mafiya samun nasara, kuma akidarsu ita ce akidar mafi yawan Musulmai a baya da yanzu, kuma akan wannan akidar jami’oin Musulmai suke karantarwa da inda suka kasance manhajinsu na akida.
Su Asha’ira ana dangantasu ne zuwa ga Imam Abul Hasan Al’ash’ary, don haka zuwa gareshi ake dangana wannan mazhaba, hakika Al’imam Al’ash’ary shi ne ya bayyana akidun salaf nagartattu kamar dai yanda lamarin ya kasance a zamanin Annabi Muhammadu SallallaHu AlaiHi Wasallam da sahabbai da tabi’ai, sannan ya kalubalanci kungiyoyi batattu sai Allah ya bayar da nasara ga mazhabin Ahalus Sunnah ta dalilinsa, Imam Murtada Az-zubaidi – Allah ya masa rahama – ya kasance yana cewa: (Idan aka tsinkayar da sunan Ahlussunnah wal jama’a to Asha’ira ake nufi da hakan da kuma Al’maturidiyyah) sannan aka kara da cewa su Asha’ira wanda shugabansu ke zama Imam Abul Hasan Al’ash’ary sun kasance martini ne ga bayyanar Mu’utazila da zantuttukansu da ba su kubuta daga wuce gona da iri da bata ba musamman a wurin masu tsanantawa a cikinsu suka tafi akai na ra’ayoyi, daga nan muke gane cewa duk wanda ya ce shi ba Ba’ash’are bane to fa – a bisa la’akari da samuwar Ash’ariyawa – to kamar ya ce shi Bamu’utazile ne.
Amma fa wanda yake siffanta Ash’ariyyawa da da cewa batattu ne wurin siffanta Allah to jahili ne ko batacce ne bai san komai ba akan akidan Ash’ariyyawa.