Fadin Bismillah lokacin cin abinci

Egypt's Dar Al-Ifta

Fadin Bismillah lokacin cin abinci

Tambaya

Mene ne hukuncin fadin Bismillah lokacin cin abinci? Mene ne kuma hukuncin wanda ya manta ya tuna bayan ya fara cin abinci?

Amsa

Fadin bismillah a lokacin fara cin abinci sunna ne; saboda Hadisin Umar Bn Abu Salma (Allah ya kara yarda da su) ya ce: Na ci abinci tare da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), sai hannu na ya fara kara-kaina a cikin kwano, sai ya ce: (Ka ambaci sunan Allah, ka kuma ci da hannun dama, ka kuma ci gabanka) [Ibn Majah da wannan ma’anar, da Abu Dawud]

Wanda kuma ya manta a farko, zai fade ta a duk sanda ya tuna, sai ya ce: “BismilLahi Awwalahu wa Ãhirahu”; saboda Hadisin da Nana A’isha Ummul muminina (Allah ya kara yarda da ita) ta ruwaito, cewa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan wani daga cikinku zai ci abinci ya ambaci sunan Allah, idan kuma ya manta bai ambaci sunan Allah a farko ba, to ya ce: “BismilLahi Awwalahu wa Ãhirahu”) [Abu Dawud].

Allah shi ne masani.

 

Share this:

Related Fatwas