Bayyanar da BismilLah a fatiha yayi...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bayyanar da BismilLah a fatiha yayin sallah.

Tambaya

Mene ne hukuncin bayyana bismillah a sallah?

Amsa

Shi bayyana bismillah a farkon fara karatun fatiha a sallah yana daga cikin mas’alolin da malamai suka samu sabani akai, domin kuwa su shafi’iyyawa tare da wasu malaman suna ganin yin hakan a matsayin mustahabbi ne a bayyana bismillah, yayin da wasunsu daga cikin malamai suna ganin boyewa shine mafi dacewa.

Wannan lamari a cikin alamomin sallah bai kai matsayin sunnoni masu karfi ba, sabanin da yake cikinsa kadan ne, kuma lamarin abune mai yalwa, duk wanda ya bayyana fatiha yayi daidai, hakanan wanda ya boye shima ya yayi daidai, don haka kowani limami sai ya kula da rashin sabawa abinda mutane suka saba dashi na zabin abinda ya yi musu na bayyana karatun bismillah ko kuma asirtawa.

Bai kamata irin wadannan mas’alolin da ake samun sabani akansu su zama ababen tayar da fitina ko raba kan musulmai ba, abinda ya kamata shine mu wadatu da abinda ya wadata magabatanmu nagartattu wurin yin ladabi a sabani da ake samunsu dashi a duk wata mas’ala da fikihu.

Share this:

Related Fatwas