Neman biyan bukata domin darajar An...

Egypt's Dar Al-Ifta

Neman biyan bukata domin darajar Annabi Sallahu Alaihi wa sallam da Alayan gidansa da Ka’aba

Tambaya

Mene ne hukuncin mutum ya zama mai bukatar waninsa domin cikan burinsa, kamar hadawa da Annabi S.A.W. da Alayen gidansa da Ka’aba?

Amsa

Neman rabauta ko tabbatar da zance tare da ambaton Annabi S.A.W. ko da waninsa kamar mutum ya ce: (Don girman Annabi) ko (Don girman Ka’aba dss) wanda ba wai yana nufin hakikanin rantsuwa ne da wadannan abubuwan da ya ambata ba, to wannan ya halasta a shari’ance babu damuwa a cikinsa wurin mafi yawan malaman fikihu, bai halasta a hana yin haka ba da hujjar da ke bayyana haramcin yin rantsuwa, wannan bai da alaka da wancan a hukunci, wannan shi ne abin da yazo cikin zancen Manzon Allah S.A.W. da zancen sahabbai ma su girma.

Daga Abu Huaraira Allah ya kara masa yarda ya ce: Wami mutum yazo wurin Annabi S.A.W. sai ya ce: Ya Manzon Allah, wace sadaka ce mafi girman lada? Sai Annabi S.A.W. ya ce: (Lallai da darajar mahaifinka sai ka ba shi labari, shi ne ka bayar da sadaka kana halin lafiya kana mai kwadayin abin da ke hannunka tare da tsoron talauci ya kamaka, kana fatan wanzuwa) har zuwa karshen hadisin.

Bukhari da Muslim sun ruwaito cewa matar Abubakar Siddik Allah ya kara yarda da su ta ce masa : (Ba haka bane hasken fuskana, ai ita yanzu a halin yanzu ta fita fiye da ninkin haka so uku). Tana nufin abincin bakinsa.

Allah Ta’ala ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas