Yiwa Annabi SallalaHu AlaiHi wasallam salati bayan kiran sallah.
Tambaya
Mene ne hukuncin yiwa Annabi SallalaHu AlaiHi wasallam salati bayan kiran sallah?
Amsa
Yin salatin Annabi sallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam bayan kiran sallah yana daga cikin abinda mafi yawan masu kiran sallah suke aiwatarwa, abu mafi dacewa shine barin mutane akan abinda suka saba kuma zuciyarsu take natsuwa da yinsa, duk wanda ya saba bayyana hakan, to babu komai, hakanan duk wanda ya saba barin bayyanawa shima haka babu komai, domin kalmomin kiran sallah sanannu ne ba a tsaron su gaurayu da yin salatin, abin lura anan shine abinda musulmi yake samun natsuwa dashi a zuciyarsa, wannan kuma bay a kawo sabani da rarrabuwa a tsakanin musulmai.
Bai kamata irin wadannan mas’alolin da ake samun sabani akansu su zama ababen tayar da fitina ko raba kan musulmai ba, abinda ya kamata shine mu wadatu da abinda ya wadata magabatanmu nagartattu wurin yin ladabi a sabani da ake samunsu dashi a duk wata mas’ala da fikihu.