Yawan umurar da Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya yi.
Tambaya
Nawane adadin ummaran da Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya yi?
Amsa
Annabi SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya yi ummara so hudu, saboda an karbo daga Anas Allah ya kara masa yarda inda ya ce ya tabbata cewa Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa Alihi wa Sallam ya yi ummara so hudu a rayuwarsa, kuma dukkansu ya yisu ne a watan Zul ki’ida in banda wacce ya yi lokacin aikinsa na hajji, wato ummararsa na Hudaibiyya a watan Zul ki’ida, sannan sai wata ummarar da ya yi a watan Zul ki’idan na shekarar da ta sagayo, sai ummarar da ya yi a Ja’aranah a inda ya raba ganimar da aka samu a Hunain a watan Zul ki’ida, sai kuma wata ummarar da ya yi a ya yin aikinsa na hajji. Muslim.