Yin algus a cikin kayan sayarwa wanda aka cimma yarjejeniyar shigowa da su.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin algus a cikin kayan sayarwa wanda akayi yarjejeniyar shigo da su a munakasat?
Amsa
Yin algus a cikin kayayyakin da aka cimma yarjejeniyar shigo da su a tsarin munakasat ko makamancin haka to haramun ne a shari’ance, kuma cin dukiyar mutane ne da barna, hakika musulunci ya haramta algus da yodara, Annabi S.A.W. ya ce: (Wanda ya ha’ince mu to ba shi daga cikin mu) {Muslim ne ya ruwaito shi}.
An umurci muminai da suka yi gaskiya kuma su kasance tare da masu gaskiya, Allah Ta’ala ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi Imani ku ji tsoron Allah sannan ku kasance tare da masu gaskiya) {At’tauba:119}.
Anyi umurni da cika alkawari tare da sharudda wurin kulla ciniki, Annabi S.A.W. ya ce: (Musulmai na gudanar da lamuransu ne bisa sharuddan da ke tsakaninsu, sai dai fa wani sharadi da ya haramta halal ko ya halarta haram) {Darul Kudni ne ya ruwaito}.
Allah Subhanahu wa Ta’ala ne mafi sani.