Cin zarafin mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Cin zarafin mutane

Tambaya

Mene ne hukuncin cin zarafin mutane da cin mutumcinsu?

Amsa

An karbo daga Sa’eed bin Zaid Allah ya kara musu yarda, daga Annabi S.A.W. ya ce: (Yana daga cikin mafi girman riba cin mutuncin mutum musulmi ba tare da hakki ba), {Ahmad da Daud ne suka ruwaito}, a cikin wannan hadisin akwai gargadi mai tsanani daga Manzon Allah S.A.W.  ga mai cin mutumcin mutane da cin zarafinsu da kutsawa cikin lamauransu, sai ya siffanta hakan da riba, ba haka ba ma, shi ne “mafi girman riba” to wannan ya hukunta zaman cin zarafin mutane kasancewa mafi munin zunubi, da tsananin laifi mai gadar da zunubi, duk wannan na nuni ne akan cewa cin zarafin mutane laifi ne babba, sakamakon cewa hakan wani abu ne da ya rataya da hakkin mutane, don haka mai aikata hakan ya cancanci narko da tsananin horo. 

Share this:

Related Fatwas