Bibiyan sirrin mutane
Tambaya
Mene ne hukuncin bibiyan sirrorin mutane da bincike akan aibobinsu?
Amsa
Lallai Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya tsananta wajen fadakar da Musulmai game da hatsarin da yake tattare da bibiyan sirrorin mutane da neman aibobinsu, inda ya bayyana wanda yake yin haka a matsayin mutumin da Allah zai keta suturar da ya yi masa idan har bai daina ba, Allah Madaukaki zai kunyata shi koda kuwa a cikin gidansa ne; an ruwaito Hadisi daga Sauban (Allah ya kara yarda da shi) daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Kada ku cutar da bayin Allah, kada kuma ku muzanta su, kada ku nemi sanin sirrorinsu; domin sun wanda ya nemi sanin sirrin dan uwansa Musulmi, to kuwa Allah zai tona asirinsa ya kunyata shi a cikin gidansa) [Ahmad].
Haka nau’i ne daga cikin nau’o’in liken asiri da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi gargadi akansa, da ma duk wani abu da yake bata dangantaka mai kyau a tsakanin mutane, yake kuma kawo kiyayya da gaba, Hadisai masu yawa ne suka zo da haka, a cikinsu akwai Hadisin Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi), daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), ya ce: (Ahir dinku da yin zato; domin shi zato shi ne mafi karya a zantuttuka, kada ku yi binciken sirrin mutane domin kawunanku, kada kuma ku binciki sirrorin mutane domin amfanin waninku, kada kuma ku yi wa junanku hasada, kada ku juya wa junanku baya, kada ku ketaci juna, ku zama bayin Allah ‘yan uwan juna) [al- Bukhari da Muslim].