Bibiyar aibobin mutane
Tambaya
Mene ne hukuncin bibiyar aibobin mutane, da cikin masu mutunci da yayata su?
Amsa
Yunkurin da wasu mutane suke yin a kutsawa cikin kebantattun rayuwar mutane da shiga cikin sirrinsu ba tare da sun sani ba, da kuma tona wannan sirri ta hanyoyi mabambanta irinsu:
Daukansu a hoto ta hanyoyin cigaban da zamani ya zo da su
Sanya masu ido a fakaice.
Satar jin maganganun da suke yi
Da sauran wasu hanyoyin na daban
Da kuma yada su a gidajen jaridu, da kafafen sadar da zumunta na zamani, da sauransu, duka wannan suna cikin bibiyar aibobin mutane, da keta alfarmansu wanda shari’a ta wajabta ba su kariya da suturtawa, duka wannan ayyuka ne masu matukar muni a wurin dukan masu hankali, haka ma a al’adance, kuma haramun ne a shari’a, dokokin kasa sun hana, duk wanda ya yi ya aikata zunubi da laifin da ya cancanci a yi masa hukuncin da zai zama izina ga sauran jama’a, wajibi ne mutum ya nesanci aikata ire- iren wadannan ayyuka masu halakarwa, saboda ya katange kansa, ya kuma katange al’umma da kasarsa.