Hakkokin masu bukata ta musamman

Egypt's Dar Al-Ifta

Hakkokin masu bukata ta musamman

Tambaya

Mene ne hakkokin masu bukata ta musamman a cikin shari’ar Musulunci?

Amsa

Ita shari’ar Musulunci ta baiwa masu bukata ta musamman muhimmanci sosai da kulawa na musamman, sai shari’a ta wajabta bin duk wasu hanyoyi na karfafa musu gwiwa da nuna musu goyon baya wurin suyi karatu, tare da sanin yanda za su iya kwarewa a fannonin rayuwa, sannan a ataimaka musu wurin gano abubuwan da suka kware akai, haka nan Musulunci ya haramta duk wata hanya ta nuna musu wariya ko nuna musu kyama, saboda ita shari’ar Musulunci ta zo ne domin kira akan taimakekeniya, haka nan ta kwadaitar da mutane akan kyawawan dabi’u, da nesantar munanan maganganu da ayyuka, don hakane ma zargi da hani suka zo akan masu yin isgilanci da yin yafice da wulakanci, kamar dai yanda ya zo cikin fadin Allah Ta’ala: (Ya ku wadanda kuka yi Imani kada wasu mutane daga cikinku suyi wa wasu mutane izgilanci ta iya yiwuwa su kasance mafi alheri akansu kada wasu mata suyi wa wasu matan daban izgilanci ta iya yiwuwa sune mafi alheri akansu ku dena yi wa kawukanku zunde kada ku rinkayi wa kawukanku lakabi mare kyau kaicon suna na fasikanci bayan Imani duk wadanda basu tuba daga haka ba to ire irensu sune azzalumai) {Hujurat:11}

Share this:

Related Fatwas