Wasu daga cikin sifofin batattun ku...

Egypt's Dar Al-Ifta

Wasu daga cikin sifofin batattun kungiyoyi da suka zo a cikin Hadisan Annabi

Tambaya

Shin Hadisan Annabi masu girma sun yi bayanai akan sifofin Hawarijawa da masu tsattsauran ra’ayi?

Amsa

Lallai Hadisan Annabi masu girma sun yi gamammiyar Magana akan wasu daga cikin sifofi, wadanda idan aka same su to a yi taka- tsantsan da masu shi, kada a bi manhajin da suke a kai; saboda su masu tsattsauran ra’ayi ne da suka fita daga karantarwar addini mai girma; an ruwaito Hadisi daga Abu Idris al- Khaulaniy cewa ya ji Huzaifatul Yamani yana cewa: Mutane suna tambayar Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) akan alhairi, ni kuma ina tambayarsa ne akan sharri gudun kada ya riske ni, sai na ce: Ya Manzon Allah, a da muna cikin jahiliyya da sharri, sai Allah ya kawo mana wannan alhairin, shin bayan wannan alhairin kuma akwai wani sharri da zai zo? Sai ya ce: na’am, sai na ce: shin bayan wannan sharrin wani alhairi kuma zai zo, sai ya ce: Na’am, sai dai a cikinsa akwai matsala, sai na ce: mece ce matsalar? Sai ya ce: mutane ne da suke bin sunnar da ba tawa ba, suke kuma bin shiriyar da ba tawa ba, z aka gane haka daga gare su, ka kuma ki haka. Sai na ce: shin bayan wannan alhairin kuma akwai wani sharri da zai zo? Sai ya ce: Na’am, masu kira ne a kofofin jahannama, duk wanda ya amsa kiransu su jefa su cikinta, sai na ce: ya Manzon Allah a sifanta mana su, sai ya ce: mutane ne da suke daga cikinmu, suna magana da harshenmu, sai na ce: ya Manzon Allah, yay azan yi idan hakan ya riske ni? Sai ya ce: ka kasance tare da al’ummar Musulmai da shugabansu, sai na ce: idan babu al’umma, kuma babu shugaba fa? Sai ya ce: ka kaurace wa duka wadannan kungiyoyin, koda kuwa z aka koma ka rungumi bishiya ce har zuwa lokacin da mutuwa za ta riskeka kana kan haka) [al- Bukhari da Muslim]

 Matsalar da ake nufi a cikin Hadisin shi ne rashin bin ingantacciyar shiriya da aka amince da ita, sakamakon cakudewar daidai da kuskure a wuri daya, kaman yanda (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (suke bin sunnar da ba tawa ba, suke kuma bin shiriyar da ba tawa ba, za ka gane haka daga gare su, ka kuma ki haka), ma’ana kana inkarin wasu abubuwa da suke aikatawa, suke kuma riya cewa su ne daidai.

Share this:

Related Fatwas