Ka’idojin amfani fa Hadisan da suka yi Magana akan fitintunu a rayuwar mutane..
Tambaya
Mene ne wajibin abin da ya kamata Musulmi ya yi game da Hadisan da suka yi Magana akan karshen zamani, kuma ta yaya kungiyoyin da suke kafirta Musulmi suka yi gangancin fassara su, da aiwatar da su?
Amsa
Nazari da duba Hadisan da suka yi Magana akan karshen zamani abu ne da ya halatta, haka ma imani da abubuwan da za su faru a cikinsu yana cikin ainihin akidar da wajibi Musulmi ya kudurce, saboda dole ya yi imani da gaibin da ya tabbata a cikin Alkur’ani da ingantattun Hadisai, sai dai saukar da wadannan Hadisan akan wasu abubuwa kebantattu abu ne da yake bukatar duba da nazari, dalilin halaccin shi ne samun wasu surori da aka bayyana cewa su ne wadanda Hadisan da suka yi Magana akan fitintunu suka yi nuni zuwa gare su, musamman a cikin rubuce- rubucen da magabata suka bari.
Saukar da wadannan Hadisai akan wasu abubuwa da suka faru abu ne da yake da sharudda da ka’idoji, Kaman ya kasance bayan faruwan abu ne ba kafinsa ba, wannan ka’ida ce da take fili a cikin ayyukan sahabbai (Allah ya kara yarda da su), Khuzaimat Bn Sabit bai bayyana “Fi’atul baghiya” ba sai bayan kasha Ammaru Bn Yasir (Allah ya kara yarda da shi), haka ma Asma’u Bont Abubakar ba ta yi wa Hajjaju da Mukhtar al- Sakafiy hukunci ba sai bayan bayyana kasha- kasha da halaka, sai ta yi wan a farko hukunci da cewa makaryaci ne, na biyun kuma mai kirkirar karya.
Saukan da wadannan Hadisai kafin faruwarsu sau da yawa yana jefa al’umma cikin matsaloli masu yawa da ba ta da bukatarsu, kuma hakan ya bude kofofin sharri da a baya duka a rufe suke, sai dai wannan tawili na kuskure da ake yi wa Hadisan Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bude su, alal misali irin yanda aka saukar da Hadisan Mahdi akan wasu ayyanannun mutane, sannan a fara ta’assubanci akansu, hakan ya kuma kai zuwa ga zubar da jinin Musulmai, da keta mutuncinsu ba tare da wani dalili ba.