Ka'idojin shari'a game da kayayyakin wasanni na zamani da ake shakatawa ta halal da su.
Tambaya
Shin akwai ka'idojin shari'a ne game da kayayyakin wasanni na zamani da ake shakatawa ta halal da su?
Amsa
Abin da shari'a mai girma ta tabbatar shi ne: asali game da kayayyakin wasanni da wargi da sanya nishadi shi ne halacci, matukar ba an gwama wasannin da wargin da abin da shara'a ta hana ba, to a nan sai a hana, saboda maganar Allah mai girma da yake cewa: (Ka hada mu da shi gobe, ya yi wasa da kai- komansa, lallai mu masu bas hi kulawa ne) [Yusuf: 12]; Imam al- Dabariy a cikin "Jami'ul Bayan" (15/570 – 571) ya ce: Ibn Abbas ya ce: (ya yi wasa ya yi kai- komonnsa..) ya yi wasa da nishadi da kai- komo.. an ruwaito Imam al- Dhahhak ya ce: Ya yi wasa ya sami nishadi.
Da shari'ar Musulunci ta halatta wasa da nishadi, ba ta bambance tsakanin wasannin yara da na manya ba, kowa da abin da ya dace da shi, amma dai kowanne yana da ka'idoji da dole ne a kiyaye su, a cikinsu akwai: Kada wasannin ya sauya daga raha ya zama koda yaushe, kada kuma ya zama yana kunshe da abin da aka haramta, irinsu caca da tashin hankali da sauransu, kada kuma wannan wasannin ya kai zuwa ga tozarta hakkokin Allah akan bayi, kaman sallah da sauransu, ko tozarta hakkokin bayi, kaman hakkokin iyali, ko yana bitar karatu da neman ilimi.