Kalubalantar tunani mai tsauri.
Tambaya
Yaya gwargwadon tasirin yaki da kungoyiyin masu tsattsauran ra’ayi da na ‘yan ta’adda yake?
Amsa
Lallai fuskantar ra’ayi na tsattsauran ra’ayi da gaske shi ne wanda zai iya kawo karshen yaduwar ra’ayin ta’addanci tun daga tushensa, kuma hakan zai taimaka wurin tabbatar da zaman lafiya a bangaren tsaro da siyasa da kuma tattalin arziki a dukkan kasashen wannan yanki da na Larabawa, wannan shi zai takaita mana yawan asara na zubar jini da yawa da asarar rayuka, wanda ke faruwa sakamakon amfani da karfin jami’an tsaro ko kuma asarar rayuka bayan hare haren ta’addanci.
Gidan bayar da fatawa ta kasar Misira tana daga cikin muhimman cibiyoyin da suka yi gaggawa wurin fara kalubalantar tsattsauran ra’ayyi da ta’addanci, sannan ya takance tana bibiyan duk irin yanda lamuran suke tafiya da hauhawansu a wannan yanki, kuma wannan gida ya yi amfani da hanyoyin fasaha na zamani a matakin kare yaduwar wannan ra’ayi ko kuma a matsakin magance mikin da wannan ra’ayi ya haifarwa al’umma.
Gidan bayar da fatawa ta kasar Misira ta dogara da wasu hanyoyi na ilimi da manhaji a matsayin wani abu mai tasiri sosai domin kalubalantar wannan ra’ayi, daga cikin hanyoyin akwai dako da bin diddigi na ilimi wanda ke bibiyan fatawowin masu kafirta mutane da masu tsattsauran ra’ayi da tasirin haka a kasashen duniya, duk fa hakan ta hanyar bibiyan abin da yake wukana ne a kafofin yada labaru da kuma dandalin sada zumunta na zamani da kuma kafofin intanet, tare da samar da sansanoni masu yawa a kafar yanar gizo domin mayar musu da martini akan shubuhohin da wadannan mutane suke yadawa ta kafofi mabanbanta.