Aikata samar da ra’ayi mai tsauri.

Egypt's Dar Al-Ifta

Aikata samar da ra’ayi mai tsauri.

Tambaya

Ta yaya ake iya samar da mutane masu kwakwalen ta’addanci a cikin al’umma?

Amsa

Lallai samuwar halayya na ra’ayi mai tsauri  ba ya kasancewa a matafiya daya, don haka samuwar ra’ayi mai tsauri ga mutumin da ya yi amanna da shi a matsayin zabi na asali abu ne mai sarkakiya, domin yana rataye ne da abubuwa da daman gaske daga waje, wanda yake da alaka da zamantakewar al’umma da sauye sauyen da ake samu a cikin yanayin da ake ciki, wanda haka ke zama wani matattara na yanayi da halayya, sannan tare da wasu abubuwa na daban da suke tattare da wasu alamomin halayyar shi kansa mai tsattsauran ra’ayin, da kuma wasu halayyarsa na dabi’unsa, duk hakan na taimakawa wurin zuga shi yin aika aika, a bisa wadancan iyakokin da aka ambata akwai samun sauyin ra’ayi zuwa ga tsattsauran ra’ayi, haka kuma sukan samar da wani yanayi na bazata ga wanda ya yi amanna da zafafawa akan komai.

Abin da ya zama wajibi a lura da shi anan shi ne bangaren sani wurin samar da alamomin ra’ayi mai tsauri wanda ke kasancewa mataki mafi rauni kuma mafi karanci wurin tasiri, shi ne   wurin samar da zahirin ta’addanci, amma wannan ba ya nuna shi ne ainihin kaskanta gudunmawar da litattafai da kafofin sadarwa na zamani suke da shi wurin yada munanan fahimta da ra’ayuyyuka, sai dai abin nufi anan shi ne tabbatar da cewa wadancan kafofin ilmantarwan su ne hanyoyin yiwa kwakwale mulkin mallaka, inda suke kokarin amfani da damarmakinsu wurin tankwara mutum a bisa tsarin zamantakewa da kuma halayya, inda hakan ke daukar matsayi na wayewarsa da hankalisa, kuma hakan ne ke bayar da daman yin tunani akai da bayyanawa duniya irin addinin da irin wannan mutumin ke aikatawa kuma ya yi Imani da ayyukan, daga nan kuma su wadancan hanyoyin su kan samu na su karfin gwiwan ne daga irin fahimtar da shi mai tsattsauran ra’ayin ya ginu a akansu.

Wata kila dalili akan haka shi ne kasancewar wadancan hanyoyin da ake sanin abubuwa da su ba sa gushewa wurin janyo ra’ayin magoya baya duk da karancinsu, amma matune masu hankali da tunani suna cigaba da kasancewa akan daidaitacciyar hanya wace take ta tsaka-tsaki.

Share this:

Related Fatwas