Kunar- bakin- wake

Egypt's Dar Al-Ifta

Kunar- bakin- wake

Tambaya

Shin kunar- bakin- waken da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke yi ya halasta a Musulunci?

Amsa

Ba boyayyen al’amari ba ne cewa ayyukan kunar bakin- wake da ‘yan ta’adda suke yi na kai wa amintattu da wadanda ba su ji ba ba su gani ba da sassan al’umma hari, haka tunanin wadannan kungiyoyin ga wadanda suka saba musu kan cewa su kafirai ne kuma sun cancanci mutuwa ko kisa tunani ne mummuna wanda ba ya nuni kan koyarwar Musulunci ko shari’ansa bayyananne, wanda ya zo domin sanya amince a zukatan mutane da wanzar da zaman lafiya da aminci ga mutanen duniya baki daya.

Hakika shari’ar Musulunci ta yi hani akan zubar da jini ta kowace fuska, Allah Ta’ala yana cewa: (Duk wanda ya kashe rai ba tare da ta kashe wata ran ba, ko kuma ya yi barna a doron kasa, to fa kamar ya kashe mutane ne baki daya, haka nan duk wanda ya raya wata rai a doran kasa tamkar ya raya mutane ne baki daya) [Alma;ida 32]

Don haka duk abin da wadannan kungiyoyin na ‘yan ta’adda suke aikatawa ya yi hannun riga da koyarwar Musulunci, wanda kare rayuka yake zama a kan gaba tare da kiyaye martabar ran, ai irin wannan aika-aikan a zahiri na kasancewa bata suna ne ga sunan Musulunci da Musulmai, saboda a cikin hakan akwai zubar da jinin Musulmai ba tare da hakki ba.

Share this:

Related Fatwas