Rashin daidaiton lokacin haila sakamakon rashin lafiya.
Tambaya
Mace wacce ba ta da lafiya da ake yi mata magani ta hanyar allurar sinadari, sannan hakan yana kawo jirkicewan hailarta, ta yaya za ta iya kirga kwanakin al’adarta.
Amsa
Idan mace ta ga jini yazo mata kafin cikan kwanaki goma da yin tsarkinta na baya, to wannan jinin yana kasancewa na istihada ne –wato jinin ciwo-, amma idan ta ga jinin amma bayan cikan kwanki goma ko fiye da haka, to jinin haila ne, idan har ya cika kwanaki uku tare da dararensu, ko fiye da haka matukar kwanakinsa ba su wuce kwanaki goma ba, kuma wannan jinin ba wai yana zuwa mata ne a bisa al’ada ba, idan kwanakin jinin suka gaza kwanaki uku tare da dararensu to jinin istihada ne, idan kuma ya haura kwanaki goma sannan kuma yakanzo mata loto-loto kafin cikan kwanaki goma, to ta koma kidayashi cikin al’adanta, domin ya zama hailarta, kuma bisa gwargwadon al’adanta, duk abin da ya karu akan haka tojinin istihada ne, a wannan lokacin sai ta rama abin da ya wuce ta na sallah gwargwadon kwanakin da suka karu kan hailarta, idan kuma ba ta yin al’ada kamar yanda aka sani, to sai a kirga zuwa karshen abin da ake iya yi na haila wato kwanaki goma, don haka sai hailarta ya kasance kwanaki goma kenan, duk abin da ya karu akan kwanaki goma to ya zama jinin istihada wato ciwo, sai ta yi wankan tsarki bayan kwanaki goma, amma idan jinin ya cigaba da zuba to anan za ta kirga kwanakin hailarta a kowani wata kwanaki goma kenan, duk abin da ya karu akan wadannan kwanakin to duk cikin tsarki take, wannan yana zuwa ne matukar ta san tsawon lokacin zuwan hailarta da adadin kwanakinsa, ta san farkonsa da kuma karshensa, idan kuma ba ta yin haila gaba daya, sai a kirga mata mafi yawan lokacin haila wato kwanaki goma, sai adadin kwanakin hailarta shi ne kwanaki goma, duk abin da ya karu akan haka to ya zama istihada, duk lokacin da ya tabbata cewa jinin nata na istihada ne, to komai ya halasta gareta wanda ya kasance ya haramta gareta a lokacin haila kamar sallah da azumi da makamancin haka bayan ta yi tsarki, sai dai fa asan cewa wannan kididdigan ya kebanci hukunce- hukuncen ibada ne na sallah da azumi da makamancin haka ba wai hukunce- hukuncen idda ba.