Rama sallah a lokacin da aka hana yin sallah
Tambaya
Shin ya halatta Musulmi ya rama sallolin da suka kubuce masa a lokutan da shari’a ta hana a yi sallah a ciki?
Amsa
Shari’a ba ta hana a rama sallolin da suka kubuce a dukan lokutan da aka karhanta yin sallah a ciki ba, hakan ba makruhi ba ne, saboda Hadisin da Sayyiduna Anas Bn Malik ya ruwaito, ya ce: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan barci ya dauke wani daga cikinku bai sami yin sallah ba, ko kuma ya manta, to ya yi sallarsa a duk sanda ya tuna, saboda lallai Allah ya ce: (Ku tsayar da sallah saboda tunani) [Muslim]. Wannan gamammen umurini na rama sallolin da suka kubuce yana nuni ne zuwa ga halaccin rama sallah a dukan lokuta, har da lokacin da aka karhanta; wannan shi ne ra’ayin jamhur din malaman Fikihu.