Taimakekeniya akan aikata alheri
Tambaya
Mene ne ladan shiga cikin aikin tadawwa’i wurin kwarfe ruwa daga kan hanyoyi saboda saukan ruwan sama?
Amsa
Taimakekeniya mai amfani tare da kwararru wurin tarayya na aikin gayya domin kwarfe ruwan kan hanya sakamakon saukan ruwan sama ta hanyar karkatar da ruwan a inda aka kebance na musamman, a cikin haka akwai lada mai yawa daga Allah Ta’ala, kwarfe ruwa daga hanyoyi zuwa inda aka kebance domin haka wani abu ne mai kyau da ake so, hakanan mutum kan samu lada mai yawa akan haka a wurin Allah Ta’ala, domin kawar da kazanta akan hanyar mutane yana daga cikin rukuni na imani, hakika malamai sun ambaci cewa manufar kawar da kazanta daga hanya shi ne: dauke duk wani abu mai cutarwa ga mutane na dutse, ko ruwan sama, ko turbaya, ko kaya, ko wani abu mai cutarwa, hakanan sare itatuwa daga wuraren da suke tsoratar da mutane, dukkan wadannan abubuwan da aka ambata suna da kyau a kuwar da su, akwai inda ma yake zama wajibi, kamar ace akwai rijiya akan hanyar mutane, kuma ana tsoron kar makaho da kananan yara ko dabbobi su fada ciki, to anan ya wajaba a cike rijiyar, ko kuma a kewayeta domin kar masu wucewa su cutu da ita.