Shan alwashi kan yin wani abu
Tambaya
Mace ce ta sha alwashin za ta yi azumi saboda Allah a ranakun litini da Alhamis har tsawon rayuwarta, sai dai fa mijinta ya hanata saboda wahalar da take sha, shin ya wajaba a gareta ta cika wannan alwashin?
Amsa
Idan mutum bai samu ikon cika alwashinsa ba na bakace to ya wajaba gareshi ya yi kaffara ta rantsuwa, matukar dai mijin yaki yarda matarsa ta yi azumi saboda wahalar da take sha, to anan ya kamata matar da yi masa biyayya, kar ta yi azumin sai ta yi kaffarar rantsuwa saboda fadin Annabi (SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam): (Duk wanda ya yi wani bakace amma bai iya cikawa ba to kaffaransa ita ce kaffarar rantsuwa) Sunan Al’kubra na Baihaki.