ma’anar istiwa a cikin hakkin Allah
Tambaya
Mene ne ma’anar istiwa’in Allah Ta’ala akan al’arshinsa?
Amsa
Yana daga cikin tabbatattun abubuwa na akidun Musulmai cewa babu wani abu da yake iya dauke Allah Ta’ala, kuma zamani ba ya iya riskansa, saboda wuri da zamani ababen halitta ne, Allah madaukakin sarki ya daukaka daga duk wani abu da zai iya kewayeshi daga cikin ababen halitta, ai shi ne wanda ya halicci komai, kuma shi ne wanda yake kewaye da komai, kudurta wannan a zuciya shi ne abin da Musulmai suka yi ittifaki akai, kuma babu wanda zai musanta hakan, hakika ma’abota ilimi sunyi bayani akan haka inda suka ce: Allah ya kasance ba tare da wuri ba, shi dai yana kasancewa ne a inda ya kasance kafin halittan wurin, kuma bai canza daga yanda yake ba.
Amma abin da ya zo a cikin Alkur’ani da Sunnah daga cikin nassoshi da suke nuni akan daukakan Allah da buwayarsa akan halittansa suna nufin: Daukakan matsayi da girmama da buwaya da rinjaye, saboda Allah Ta’ala ya tsarkaka daga dukkan kamanceceniya da ababen halitta, kuma siffarsa ba irin ta mutane bace, daga cikin siffofin Mahalicci babu wacce ta yi kama da abin halitta na tawaya, ai shi Allah Ta’ala ya daukaka daga siffofi tawayayyu da kuma sunayensa kyawawa, dukkan abin da ya zo a tunaninka na kamannin Allah to ya saba da hakan, kuma gazawa wurin riskan abu shima riska ne, kuma bincike akan zatin Allah tsantsagwaron shirka ne.
Hakika ancewa Yahya bin Mu’az Ar-Razy: Ka bamu labari akan Allah Ta’ala, sai ya ce: Allah daya ne, sai akace masa: ta yaya yake? Sai ya ce: Mai mulki ne kuma mai iko, sai akace masa: Ina yake? Sai ya ce: Yana a madakata. Sai mai tambaya ya ce: ban tambayeka akan haka ba? Sai ya ce: Abin da ya kasance akasin haka sifa ce na ababen halitta, amma siffarsa ita ce wanda na baka labari akansa.