Iddar macen da mijinta ya rasu

Egypt's Dar Al-Ifta

Iddar macen da mijinta ya rasu

Tambaya

Ya ya iddar macen da mijinta ya rasu yake? Shin ya halasta ta rinka fita kafin cikan wa’adin iddar?

Amsa

Iddar macen da mijinta ya rasu shine watanni hudu da kwanaki goma na lissafin hijira, saboda fadin Allah Mai girma: (Wadanda suka rasu daga cikinku “mazajen aure” sannan suka bar mataye a bayansu to matan za su yi zaman idda na tsawon watanni hudu da kwana goma) [Albakra: 234].

Ya halasta ga matar da take yin idda ta fita daga gidan mijinta- wanda ya rasu – a yini, tare da kiyaye kwana a gidan mijin nata har tsawon kwanakin idda.

Allah Mai girma da daukaka ne mafi sani.

Share this:

Related Fatwas