Takura wa ‘yan mata da maganganu ko ayyukan shashanci
Tambaya
Mene ne matsayar shari’ar Musulunci game da takura wa ‘yan mata da maganganu ko ayyukan shashanci?
Amsa
Lallai shari’ar Musulunci mai daraja ta yi gargadi game da keta alfarmar abubuwan masu daraja da mutunci, ta kuma munanta aikata haka, kaman yanda ta bayyana azaba mai tsananin da take jiran wanda yake aikatawa, ta kuma bayyana irin girman wannan laifi da wurin Allah Madaukakin Sarki; saboda hakan yana rataye ne da hakkokin bayin Allah, sai Musulunci ya shelanta yin yaki da duk wanda yake aikata wanan laifi –na takura wa ‘yan mata da maganganu ko ayyukan shashanci- ya kuma yi alkawarin azaba mai tsanani a duniya da lahira ga duk wanda yake aikata haka, ya kuma wajabta wa shugabannin al’umma wajibcin fito- na- fito da wannan kazantaccen laifin da karfi babu sani babu sabo; saboda haka ne ma dokokin ukuba suka bayyana cewa aikata hakan laifi ne, da aka tanadi ukuba mai tsanani ga wanda yake aikata wannan mummunar dabi’a, kuma abin kunya.