Bin dokokin da suke tsara gudanar da aiki
Tambaya
Shin dole ne a bi dokoki da tsare- tsaren gudanar da aiki?
Amsa
Lallai abin da yake iyakance dangantaka tsakanin ma’aikaci da mai aiki a cikin tsarin jinga shi ne yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsu, wajibi ne kowanne daga cikinsu ya kiyaye abubuwan da dokokin wannan yarjejeniya ta kunsa, da kula da yanda take da sharuddanta, tare kuma da la’akari da dokoki da tsare- tsaren da suke tsara yanda za a gudanar da ayyuka, daidai da tabbatar da maslahohin dukan bangarori biyu, saboda umurni na bai daya wajen cika alkawurra.