Rama sallolin da suka wuce a halin gaggawa da jinkiri.
Tambaya
Lokaci mai tsawo ya wuce mini wanda banyi sallah a cikinsa ba, sannan na tuba zuwa ga Allah Ta’ala, Kuma ina son na rama wadannan sallolin da suka kufcemin, ta yaya zan ramasu?
Amsa
Ya wajaba ga wanda yabar salloli na farilla ya rama su a wannan ranar da ya bari, kuma a jere sai dai fa idan sunfi biyar, idan suka wuce hakan da yawa to sai ya rama wacce ta wuce a daidai lokacin da yake yin ta lokacin, saboda fadin Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Bashin Allah shine mafi dacewa na a biya) Anyi ittifaki akansa, hakanan fadin SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: (Duk wanda ya manta wata sallah to ya ramata idan ya tuna da ita, babu hanyar ramata sai dai ta wannan hanyar) anyi ittifaki akan wannan hadisin.