Maganin shaye- shaye

Egypt's Dar Al-Ifta

Maganin shaye- shaye

Tambaya

Mene hukuncin neman taimakon kwararru wajen magance shaye- shaye?

Amsa

Lallai neman taimakon kwararru wajen magance shaye- shaye abu ne da shari’ar Musulunci ta bukata, wajibi ga mai hankali shi ne kada ya mika kansa wajen neman lafiya ga wand aba kwararre ba, cikin mutanen da suke riyawa kawunansu cewa sun san komai; lallai yin wasa da rayuwar mutane, da cutar da lafiyarsu, ta hanyar daura su akan magunguna na karya, aiki ne da yake cikin ayyukan da barna ne a bayan kasa, ya kuma yi hannun- riga da irin yanda Musulunci yake matukar kwadayin ganin ya bai wa rayuwar bil’adama kariya, ta hanyoyi mabambanta, da suka hada da kiyaye ta, da kuma hana yi mata kowane irin ta’addanci, sifanta magani ga mara lafiya yana cikin ayyukan likita, sam bai halatta wand aba likita bay a yi kumajin bai wa mara lafiya magani.

 

Share this:

Related Fatwas